Yan Boko haram sun sha kai hare hare a Abuja birnin Tarayyar Najeriya REUTERS
Jami’an tsaron farin kaya a Najeriya sun ce sun gano wani wurin da mayakan Boko haram ke shirin kulla kai hare hare a babban birnin Tarayya Abuja. wannan kuma na zuwa ne a yayin Ofishin jekadancin Amurka ya yi gargadin cewa ana shirin kaddamar da hare haren ta’addanci a wasu wuraren da Turawa ke sauka.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar tace, sun samu haske ne daga wadanda aka kama da suka gudo daga yankin arewa maso gabashin Najeriya zuwa Abuja kan inda ake kulla kai hare-haren.
A cikin sanarwar hukumar ta zayyana sunayen ‘yan Boko haram da ta kame a Abuja wadanda suka jagoranci kai hare-hare a Jihohin Yobe da Filato da Kano da kuma Kaduna.
Ofishin jekadancin Amurka a Najeriya yace ya samu labarin ana shirin kai hare-haren ta’addanci a wasu mayan wuraren da ‘Yan kasashen waje ke sauka, sai dai ba tare da bayyana lokacin da za a kai hare-haren ba.
Ofishin jekadancin ya gargadi Amurkawa su yi taka-tsantsan a wuraren da suka sauka.
A watan jiya kimanin mutane 20 aka kashe a wata babbanr Otel a birnin Bamako na kasar Mali, Inda yawanci Turawa ke sauka.
No comments:
Post a Comment