Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta bankado karin lalatar da dakarun Turai suka yi da yara a Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya.
Babban jami'in kare hakkin bil Adama na Majalisar Zeid Ra'ad Al Hussein, ya ce an yi lalata da yaran ne a kusa da wani sansanin 'yan gudun hijira da ke filin jiragen sama na Bangui.
Masu bincike na Majalisar sun ce wata yarinya 'yar shekara bakwai ta shaida musu cewa, sojojin Faransa sun yi lalata da ita kafin a bata ruwa da biskit.
Mista Zeid ya ce lamarin ya faru ne a shekarar 2014, amma bai fito fili ba sai a 'yan makonnin nan.
PLACE YOUR ADS HERE
Saturday, 30 January 2016
Dakarun Turai sun yi lalata da yara a CAR'
Saturday, 12 December 2015
Mugabe ya yi katobara
Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ya sake yin wata kwaba, inda ya karanta wani jawabin da ba shi da alaka da wani taron ya halarta.
Shugaba Mugabe ya karanta jawabin ne a wajen taron shekara-shekara na jam'iyyar Zanu-PF mai mulkin kasar, kuma sai da ya ci kusan rabin minti yana karanta jawabin kana aka sauya masa da jawabin da ya dace da taron.
A watan Satumban da ya wuce ma, shugaba Mugaben ya karanta wani tsohon jawabi a majalisar dokokin kasar, wanda ya taba karantawa a baya, kimanin wata guda.
TALLA
A jawabinsa na taron jam'iyyar Zanu-PF din, Mista Mugabe ya bukaci 'ya'yan jam'iyyar da su daina fada su-ya-su a kan wanda zai gaje shi wajen mulkin kasar ta Zimbabwe.
Monday, 7 December 2015
Za a karawa sojoji wa'adin murkushe Boko Haram
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta karawa sojojin kasar wa'adin da ya dibar musu na murkushe kungiyar Boko Haram.
A kwanakin baya ne dai shugaban ya bai wa sojojin umarnin kawar da kungiyar kafin karshen watan Disambar da muke ciki.
Sai dai a wani taron manyan jami'an rundunar sojin kasar da aka yi a birnin Dutse na jihar Jigawa, Babban Hafsan tsaron Najeriya, Janar Abayomi Gabriel Olonishakin, wanda ya karanta jawabin Shugaba Buhari, ya ambato shi yana cewa a shirye gwamnatinsa take ta kara wa sojojin wa'adi idan suka bukaci hakan.
TALLA
Kungiyar ta Boko haram dai ta kashe dubban mutane, sannan ta kori miliyoyin mutane daga gidajensu, musamman a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.
Lafiyata kalau - Adam A. Zango
Jarumin fina finan nan Hausa Adam A Zango ya ce lafiyarsa kalau sabanin jita-jitar da ake yadawa cewa an yi mi shi duka.
Jarumin ya karyata jita-jitar da ake yadawa a dandalin sada zumunta na intanet a inda ake yada labarin cewa barayi sun jikkata shi a sakamakon dukan da suka yi masa.
Shahararren mawakin ya kara da cewa hotunan da ake yadawa da raunuka a jikinsa na fim din Basaja ne wanda ake yi masa kwalliya, ba raunin gaske ba ne. Ya kuma yi kira ga masu kirkirar irin wadannan karai rayi da su daina.
Sunday, 6 December 2015
Abinda Burtaniya ta ke bai dace ba_ Assad
Saturday, 5 December 2015
An gano inda ‘Yan Boko Haram ke kulle-kullen kai hari a Abuja
Yan Boko haram sun sha kai hare hare a Abuja birnin Tarayyar Najeriya REUTERS
Jami’an tsaron farin kaya a Najeriya sun ce sun gano wani wurin da mayakan Boko haram ke shirin kulla kai hare hare a babban birnin Tarayya Abuja. wannan kuma na zuwa ne a yayin Ofishin jekadancin Amurka ya yi gargadin cewa ana shirin kaddamar da hare haren ta’addanci a wasu wuraren da Turawa ke sauka.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar tace, sun samu haske ne daga wadanda aka kama da suka gudo daga yankin arewa maso gabashin Najeriya zuwa Abuja kan inda ake kulla kai hare-haren.
A cikin sanarwar hukumar ta zayyana sunayen ‘yan Boko haram da ta kame a Abuja wadanda suka jagoranci kai hare-hare a Jihohin Yobe da Filato da Kano da kuma Kaduna.
Ofishin jekadancin Amurka a Najeriya yace ya samu labarin ana shirin kai hare-haren ta’addanci a wasu mayan wuraren da ‘Yan kasashen waje ke sauka, sai dai ba tare da bayyana lokacin da za a kai hare-haren ba.
Ofishin jekadancin ya gargadi Amurkawa su yi taka-tsantsan a wuraren da suka sauka.
A watan jiya kimanin mutane 20 aka kashe a wata babbanr Otel a birnin Bamako na kasar Mali, Inda yawanci Turawa ke sauka.